(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Tanzania ta sanar da hukumar lafiya ta duniya cewa babu gaskiyar akan bullar cutar Ebola a kasar.
A ranar 14 ga watan Satumba ne dai hukumar lafiya ta duniyarWHO, ta karbi sanarwar daga gwamnatin kasar Tanzania, bayan da aka watsa jita-jitar mutuwar mutum daya daga cutar Ebola.
A farkon wannan watan ne dai wata mace ta mutu daga wata cuta wacce ba a kai ga tantance ta ba, lamarin da ya sa ake yada jita-jitar da cewa cutar Ebola ce.
Sanarwar ta hukumar lafiya ta duniya, WHO, ya zo ne kwana daya bayan da jami’in kiwon lafiya na kasar Amurka ya ziyarci kasar Tanzania bisa umarnin Alex Azar wanda shi ne shugaban hukumar kiwon lafiya ta Amurka.
Azar ya soki kasar Tanzania saboda rashin yin musayar bayanai akan mutuwar mutum guda a kasar, sai kuma wasu biyu da su ka kamu da cutar ta Ebola.
Azar ya kuma yi kira ga kasar ta Tanzania da ta aiki da dokokin kasa da kasa na musayar bayanai akan kiwon lafiya domin tantancewa.
Sai dai ministar kiwon lafiya na kasar Tanzania Ummy Mwalimu ta kore cewa an sami bullar Ebola a cikin kasar.
/129
21 Satumba 2019 - 06:58
Lambar labari: 976977
Gwamnatin kasar Tanzania ta sanar da hukumar lafiya ta duniya cewa babu gaskiyar akan bullar cutar Ebola a kasar.